Algeria
Mutane 44 sun mutu sanadiyar tsananin sanyi a Algeria
Tsananin sanyi da ake yi a kasar Algeria, ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 44, cikin mako guda. Al’amarin da ya sa al’ummar kasar ke kokawa, kan yadda gwamnatin kasar ke yin halin ko in kula da matakan gaggawa da ake bukatar dauka.
Wallafawa ranar:
Talla
Wani gidan radiyon kasar yace mutane 30 ne suka mutu sakamakon hadurran mota da ke da alaka da rashin kyawun yanayi, yayin da wasu 14 suka mutu saboda rashin lafiyan da ke da dangantaka da sanyi da dussar kankara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu