Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta dauki alhakin harin Bututun mai a Niger Delta

Kungiyar Dake ikrarin kare ‘Yancin Niger Delta ta MEND a Najeriya, ta dauki alhakin kai hari kamfanin hakar man AGIP, inda take cewa wannan wani somin tabi ne kan hare haren da ta shirya kai wa anan gaba.

Wata Mata tana Tafiya saman Bututun mai a Yankin Niger Delta a Najeriya
Wata Mata tana Tafiya saman Bututun mai a Yankin Niger Delta a Najeriya Reuters
Talla

Kungiyar ta zargi shugaban Najeriya da almubazzaranci da kudaden Gwamnati wajen bai wa tsoffin masu tayar da kayar baya a Yankin, maimakon karkata akalar kudaden wajen magance matsalar da ke addabar Najeriya.

Kungiyar tace zata kaddamar da hare hare kan kamfanin Afrika ta kudu da suka hada da MTN, da kamfanin man SACOIL, saboda abinda suka kira Jacob Zuma yana masu zagon kasa wajen hana su cim ma biyan bukatunsu.

Sai dai a bangaren gwamnati Lt Col Timothy Antigha ya mayar da martani inda ya ke cewa sun samu labarin wata kungiya da ke kira kanta MEND, ta dauki alhakin kai hari kamfanin Agip, a cewarsa suna tabatar wa kamfanonin mai da mutanen da ke Yankin Niger Delta cewa, zasu yi iya bakin kokarinsu domin tabbatar da tsaron da ya dace tare da dakili aikin kungiyar.

An kwashe tsawon shekaru Kungiyar MEND tana yi wa masana'antun mai zagon kasa a yankin Niger Delta. Sai dai an samu saukin hare hare bayan da kungiyar ta karbi afuwar da gwamnatin Ummaru Musa ta yi wa ‘Yayanta a shekarar 2009.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.