Isa ga babban shafi
Najariya

Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar durkusar da Najeriya

Al’ummar Najeriya da kungiyoyin kwadago sun yi tir da Allah waddai da matakin gwamnatin kasar na cire tallin Man Fetir wanda sanadiyar cire tallafin farashin mai ya ribanya farashin da ‘yan kasar ke sayen Man. Akan haka ne kungiyar Kwadago ta yi barazanar yin fito na fito da matakin cire Tallafin. 

Layin masu neman Man Fetur a Najeriya
Layin masu neman Man Fetur a Najeriya Nigerian Leadership
Talla

A jiya lahadi ne farkon sabuwar shekarar 2012 Gwamnatin Najeriya ta sanar da cire tallafin man fetur, abinda ya daga farashin man zuwa naira 145 kowacce ganga, wato Karin sama da kashi 100 na abinda ake saida shi ada.

Hukumar dake kula da farashin man, ta sanar da matsayin gwamnati kasar, inda tace daga yanzu Gwamnatin ta cire tallafin da take sanyawa talakawan kasar.

A bangare daya kungiyar kwadagon kasar, ta sanar da sanya kafar wando daya da Gwamnatin, inda tace nan bada dadewa ba, zasu sanar da yajin aiki, inda suka gargadi jami’an tsaro cewar, duk wanda ya musgunawa wani, zai gamu da fushin shari’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.