Isa ga babban shafi
Benin-Nijar-Cote d'Ivoire

Kasashe biyar masu amfani da harshen Faransanci sun gana a Benin

Shugabannin Kasashen Cote d’Ivoire da Benin da Togo da Burkina Faso da Nijar, sun gudanar da wani taro a Cotonou, a wani yunkurin hadin kai don samar da tsaro tsakanin kasashen Yammacin Afrika da ke amfani da harshen Faransanci.

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara yana gaisawa da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaoré.
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara yana gaisawa da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaoré. © AFP/ Ouoba Yempabou Ahmed
Talla

Shugaban Kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara ya bayyana farfado da kungiyar a matsayin wani babban mataki, inda kasashen suka yi alkawarin aiki tare.

Kasashen suna kokarin farfado da kungiyar ne da aka samar a shekarar 1959 bayan watsi da lamurran kungiyar saboda rashin dorewar tafiyar da mulkin kasashen.

Kasashen biyar sun sha alwashin aiki tare domin yaki da ‘Yan fashin jiragen ruwa da ke barazana ga kasashen na yammaci musamman kasar Jamhuriyyar Bennin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.