Isa ga babban shafi

Farfesa Wole Soyinka na goyon bayan shugaban hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Attahiru Jega

A yayin da ake cigaba da takaddama kan shirin zaben Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana goyan bayanshi ga shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, Farfesa Attahiru Jega, inda ya bukaci yan Najeriya da su yi hakuri. Ga dai abinda yake cewa:“Mu ‘yan Najeriya, Allah ya yi mana rashin hakuri, kuma wasu daga cikin mu basu da tunani, idan ka duba cin hancin da ya dabaibaye hukumar zabe a karkashin shugaban da bana so in fadi sunan shi, ka san cewa a kwai gagarumin aiki wajen maida al’amura dai-dai, amma a kwai sauran aiki wajen share dattin da Tsohon shugaban hukumar zabe ya bari, da kuma yan siyasar da ke neman cigaba da abinda su ka saba, kuma suna iya komai dan yin zagon kasa ga Farfesa Jega.” 

Farfesa Wole Soyinka na Najeriya
Farfesa Wole Soyinka na Najeriya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.