Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Tarayyar Afrika zata sake sabon shirin shiga tsakanin rikicin siyasar Cote d'Ivoire

Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana sabon shirin shiga tsakani domin magance rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire.Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz, da kasarsa ke shugabanci kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar, ya bayyana kafa wani kwamitin shugabannin kasashe, wadanda zasu shiga tsakani, cikin wata guda, kuma duk abunda kwamitin ya amince, za a aiwatar da shi.Kasar ta Cote d’Ivoire wadda ke kan gaba wajen arzikin Cocoa, rikicin shugaban na neman kassara ta, bayan zaben watan Nowamba, da duniya ta amince Alassane Ouattara ya lashe, amma Laurent Gbagbo ya ci gaba da zaman kan madafun iko, da taimakon rindinar sojan kasar. Tarayyar ta Afrika ta ce zata taimakawa Ouattara ya karbi madafun iko.

Birnin Abidjan na Cote d'Ivoire wanda rikicin siyasa ya dabaibaye
Birnin Abidjan na Cote d'Ivoire wanda rikicin siyasa ya dabaibaye REUTERS / Luc Gnago
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.