Isa ga babban shafi
Niger

An cafke manyan habsoshin soja hudu

Jami’an tsaron kasar Janhuriyar Niger sun cafke manyan habsoshin sojan kasar hudu da ake zargin na shirin kifar da gwamnati.Wata majiyar fadar shugaban kasar ta bayyana cewa ranar Asabar aka cafke mutun na hudu Lt Col Sanda Boubacar, wanda yake mamba cikin majalisar soja mai mulki.Tunda fari an cafke Col Abdoulaye Badie mutun na biyu cikin gwamnatin mulkin sojan, da Lt Col Abdou Sidikou da Col Amadou Diallo, wadanda ake ci gaba da gudanar da bincike akan abunda suke niyar aiwatarwa.Cikin watan Febrairu sojojin kasar ta Janhuriyar Niger karkashin General Salou Djibo suka kifar da gwamnatin kasar, sakamkon rikicin siyasar da ya ritsa da kasar.Sojojin sun yi alkawarin mayar da kasar bisa tafarkin demokaradiya cikins ehka shekara mai zuwa, amma akwai baraka tsakaninsu, saboda akwai masu neman ci gaba da zama kan madafun ikon kasar. 

Le général Salou Djibo à Niamey.
Le général Salou Djibo à Niamey. AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.