Isa ga babban shafi
Najeriya

Atiku ya shiga takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abubakar, ya bayyana shirin sa na takarar shugabancin Nigeria, a karkashn tutar Jam’iyar PDP, kwanaki biyu bayan Jam’iyar tace bai kammala ka’idodin komawa cikin ta ba.Yayin da yake gabatar da kansa wa Yan kasar a Abuja, Abubakar yace lokaci yayi da Yan Nigeria zasu kaucewa wadanda basu shirya tafi da kasa ba, dan baiwa kwararru irinsa, damar jan ragamar Nigeria.Tsohon mataimakin shugaban, yace shi yafi dacewa ya jagoranci Nigeria, saboda kwarewar da ya samu na rike mukamai dabam dabam, da kuma ofishin mataimakin shugaban kasa na shekaru takwas.Yayin da ake wannan, Jam’iyar PDP ta kasa, da kuma ta Jihar Adamawa, tare da Gwamnan Jihar, Murtala Nyako, sun nesanta kansu daga takarar mataimakin shugaban kasar. 

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar Rfi HAUSA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.