Isa ga babban shafi
DR Congo

Bukin Cika Shekaru 50 Da Samun 'Yancin Kai

A yau din nan ne ake ruguntsumin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kan kasar Demokradiya ta Congo, inda cikin manyan baki dake halartan bukin akwai Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Kimoon da Sarkin Kasar Belgium King Albert 11 da wasu Shugabannin kasashen duniya 18.Cikin abubuwan da akeyi yanzu haka akwai faretin musamman inda sojoji 15,000 da tankunan yaki na soja 400 suke nuna karfinmu.Taken kasar dai na neman mutanen kasar su zauna lafiya don gina kasar ne, to amma an sami lokaci mai tsawo akasar babu zaman lafiya, saboda yawaitan yaki da alamarin cin hanci da rashawa.Shekaru hudu bayan hawa kujeran mulkin kasar da  Shugaba Joseph Kabila yayi, kashi 2/3 na mutanen kasar miliyan 60 na fama da halin kuncin rayuwa.Joseph Kabila wanda ya gaji mahaifinsa da aka bindige, na fuskantar matsin lamba daga kungiyoyi daban-daban dake ja da tsarin sa na tattalin arziki da kuma batun take hakkin dan adam.A jawabin da yayi Shugaban kasar Joseph Kabila ya nemi mutan kasar dasu yi kokarin  gyatta halayen su. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.